Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Bianca Odumegwu-Ojukwu a matsayin ministar harkokin wajen ƙasar, bayan murabus ɗin Yusuf Tuggar, wanda ya ajiye mukaminsa domin shiga takara a zaɓen 2027.
Bianca ita ce ƙaramar minista a ma’aikatar kafin wannan sabon matsayin.
Kamar yadda wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ta bayyana, an kuma naɗa Sola Enikanolaiye a matsayin ƙaramin minista a ma’aikatar, inda za a jira amicewar majalisar dattawa.
Rasha za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara saboda fargabar hari daga Ukraine
Kotu ta hana INEC amincewa da tarukan da ADC ta gudanar na tsagin David Mark
Kafin a naɗa shi muƙamin, Enikanolaiye wanda haifaffen jihar Kogi ne, shi ne babban mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan harkokin ƙasashen waje.
