Home LabaraiRasha za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara saboda fargabar hari daga Ukraine
Rasha

Rasha za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara saboda fargabar hari daga Ukraine

Rasha ta sanar da cewa za ta rage girman faretin sojinta na shekara-shekara da ake yi a birnin Moscow, inda za a rage yawan sojoji, kana ba za a yi bajakolin tankuna yaƙi ko makamai masu linzami ba.

Tana gudanar da wannan biki ne domin tunawa da nasarar da ta samu a Yaƙin Duniya na Biyu, amma a ‘yan shekarun nan Shugaba Vladimir Putin ya riƙa amfani da shi wajen nuna ƙarfin sojojin kasar.

A cewar wakilin BBC, jami’an ma’aikatar tsaron ƙasar na fargabar Ukraine za ta iya kawowa bukin faretin sojin hari ta hanyar amfani da jirage mara matuƙi.

Shi ma mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce ba za a haɗa da manyan makamai a faretin bana ba, domin rage abin da ya kira barazanar hare-haren ta’addanci daga Ukraine.

Related Articles

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   6   =