Home LabaraiAmurka na tuhumar gwamna a Mexico da safarar miyagun ƙwayoyi
Amurka

Amurka na tuhumar gwamna a Mexico da safarar miyagun ƙwayoyi

Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta ce ta tuhumi gwamnan jihar Sinaloa na kasar Mexico, mai ci – da laifin zargin hada baki da shugabannin kungiyar Sinaloa mai safarar miyagun kwayoyi, domin safarar tarin kwayoyi.

Baya ga Rúben Rocha Moya, akwai kuma wasu jami’an na Mexico su tara – wadanda suke rike da mukamai a yanzu da kuma wadanda suka sauka, da su ma aka tuhuma.

Wakilin BBC ya ce a tsakiyar wannan tuhuma ta gwamnatin Trump, shi ne zargin cewa Mista Rocha na amfani da wani bangare da kungiyar ta Sinaloa domin a zabe shi Wannan, wata babbar tuhuma ce da Amurka ta yi a kan safarar miyagun kwayoyi, wadda za ta iya kara tsamin dangantaka tsakaninta da Mexico.

Shi dai gwamnan da wannan tuhuma ta shafa – Mr Rocha,wanda dan jam’iyyar Shugaba Claudia Sheinbaum ne, Morena, ya musanta tuhumar.

Related Articles

Leave a Comment

Prove your humanity: 8   +   10   =