13
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine na dab da zuwa ƙarshe, duk da cewa har yanzu ana cikin mawuyacin hali.
Putin ya bayyana hakan ne bayan bikin cika shekaru 81 da nasarar tsohuwar Tarayyar Soviet a Yaƙin Duniya na Biyu. Ya ce duk da goyon bayan ƙasashen yamma ga Ukraine, Rasha ba ta rushe ba kamar yadda wasu suke fata.
A lokaci guda, Rasha da Ukraine sun fara tsagaita wuta na kwanaki uku tare da cimma yarjejeniya kan musayar fursunonin yaƙi 1,000.
Shugaban na Rasha ya kuma zargi Ukraine da kasa amincewa da wata yarjejeniyar musayar fursunoni da Moscow ta gabatar tun ranar 5 ga Mayu.
Putin ya ce a shirye yake ya gana da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, amma sai bayan an samu ci gaba mai ma’ana wajen cimma yarjejeniyar zaman lafiya mai dorewa.
Haka kuma ya yaba da ƙoƙarin shugaban Amurka, Donald Trump, na taimakawa wajen sasanta rikicin.
Rasha ta fara mamaye Ukraine a ranar 24 ga Fabrairu, 2022, lamarin da ya haddasa mummunan rikicin da ke ci gaba har yanzu.
