A cikin wata sanarwa da hukumar dake kula da kafafen yaɗa labaru ta ƙasar fitar a gidan talabijin na kasar, ta ce kafafen da aka dakatar sun yi ta yada labarun da ka iya yin illa ga zaman lafiyar jama’a da hadin kan kasa da kuma zaman lafiyar hukumomin Nijar.
Kafofin da aka dakatar sun hada da gidan talabijin na France 24, gidan Radio France International da France Afrique Media, da LSI Africa, da kamfanin dillancin labaru na AFP, da TV5 Monde, da TF1 Info, sai kuma Jeune Afrique da kuma Mediapart.
Saƙon sanarwar Ya ce dakatarwar ta fara aiki “nan take” kuma an rufe “duk wasu kafofi na tauraron dan adam, da hanyoyin sadarwa, da dukkanin hanyoyi sadrwa na zamani wato digital da na yanar gizo, da kuma kafofin manhajojin wayar hannu.
Malalar Mai a tsibirin Kharg sama da murabba’in kilomita 52 saman tekun Fasha
Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum da shida cikin mutanen Ngoshe da aka sace
In ba a mance ba tun a watan Yulin shekarar 2023 aka dakatar da ayyukan gidajen yaɗa labaru na Radio Faransa da na France24 daga yaɗa shirye-shiryensu a Jamhuriyar Nijar, kwanaki kaɗan bayan da sojojin ƙasar suka mulki.
