Bayanai daga ƙungiya mai kula da sa ido da kuma amfani da na’urorin hangen nisa kan malalar mai da aka sani da Orbital EOS, ta na mai cewa, an saki gangar mai sama da 3,000 a cikin Tekun Fasha.
Duk da cewa har yanzu ba a san ainihin musabbabin malalar wanan mai ba, wasu na danganta shi da hare-haren jiragen sama da Amurka da Isra’ila suka kai a ‘yan makonnin nan, waɗanda ƙila sun lalata bututun mai.
Wasu na kuma bayyana cewa,da alama mai na malala ne daga tsofin jiragen ruwa da yanzu haka aka dakatar da su biyo bayan rufe mashigin Hormuz.
Bangaren hukumomin Teheran,ba su ce ufon ba,kazzalika masu tsaron gabar ruwan ƙasar ta Iran sun kaucewa magana a kai.
Yanzu haka malalar mai na gudu zuwa ruwan Saudiyya.
Masana sun bayyana damuwa,inda suka yi gargadin cewa ko da malalar mai ba ta da yawa,za ta iya yi ɓarna ga muhalli wanda zai shafi duniya.
