Home TsaroSojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum da shida cikin mutanen Ngoshe da aka sace
Sojojin

Sojojin Najeriya sun kuɓutar da mutum da shida cikin mutanen Ngoshe da aka sace

Rundunar Sojojin Najeriya ta tabbatar da kuɓutar da wasu mata uku da yara uku cikin mutanen Ngoshe da mayaƙan Boko haram suka sace a farkon watan Maris.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar Operations Hadin Kai mai yaki da Boko Haram, Laftanal Kanal Sani Uba ya fitar ya ce sojojin sun kuɓutar da mutane shida a garin Amuda da ke tsakanin garin Ngoshe da Gava lokacin da suke sintiri.

Sanarwar ta ƙara da cewa mayaƙan sun buɗe wa sojojin wuta da nufin kwace mutanen, sai dai sojojin mun mayar da martani cikin ƙwarewa lamarin da ya tilasta wa mayaƙan janyewa zuwa tsaunukan Mandara.

Laftanal Kanal Sani Uba ya ce cikin waɗanda aka kwato har da wata da aka tilasta wa auren ɗaya daga cikin kwamandojin mayaƙan.

Sojojin sun kuma buƙaci al’umma su rika taimaka musu da bayanan sirri domin daƙile hare-haren mayaƙan na Boko Haram

Related Articles

Leave a Comment

Prove your humanity: 10   +   1   =