Home TsaroAmurka ta sayar da makaman kusan dala biliyan 9 ga ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya
Amurka

Amurka ta sayar da makaman kusan dala biliyan 9 ga ƙawayenta a Gabas ta Tsakiya

Ma’aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da sayar da makaman soji da kuɗinsu ya kai dala biliyan 8.6 ga ƙawayenta ƙasar da ke Gabas Tsakiya, da suka haɗa da Isra’ila da Qatar da Kuwait da kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Matakin na zuwa ne yayin da ake cikin mako na uku da fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar yaƙin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Daga cikin waɗannan makaman an sayar wa Qatar na fiye da dala biliyan 4, yayin da aka sayar wa Kuwaita na dala biliyan 2.5, sai kuma Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da ta samu na dala miliyan 147.

Related Articles

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   6   =