Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince tare da bayar da umurnin bai wa sabbin jakadun da ya naɗa filaye a babban birnin ƙasar Abuja.
Ministan babban birnin ƙasar Barr Nyesom Wike ne ya sanar da umurnin shugaban ƙasar a yau Laraba, a lokacin wata ziyarar aiki da sabbin jakadun suka kai mishi, bisa jagorancin babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Ambasada Dunoma Umar Ahmed.
Wike ya bayyana cewa an ɗauki matakin ne da nufin samar wa jakadun wuraren zama na din din din a babban birnin ƙasar, tare da tabbatar da cewa suna da masauki a lokacin da suka dawo Najeriya domin bai wa shugaban ƙasar bayanai game da aikinsu da kuma bayan sun kammala aiki.
Ministan Abujan ya kuma buƙace su da su kasance ido da kuma kunnen Najeriya a yayin da suke aikinsu, inda ya jaddada cewa hallayarsu da yadda suka wakilci ƙasar zai nuna yadda duniya za ta kalli ƙasar.
