Home LabaraiAna gudanar da zanga-zangar ƙin baƙin hauren da ke zaune a Afirka ta kudu ba bisa ƙa’ida ba

Ana gudanar da zanga-zangar ƙin baƙin hauren da ke zaune a Afirka ta kudu ba bisa ƙa’ida ba

Ana gudanar da zanga-zangar ƙin baƙin haure da ke zaune a Afirka ta kudu ba bisa ƙa’ida ba a birnin Johannesburg.

Daruruwan masu zanga-zangar sun taru suna rera waƙoƙi, yayin da suke tattaki ta tsakiyar birnin zuwa ofisoshin gwamnati.

Zangar-zangar, wanda wata ƙungiyar masu adawa da ƴan ci rani ta shirya, na cikin wani gagarumin kamfe da ke kiran a tsaurara matakai kan ƴan kasashen waje marasa takardun zama.

Ana kara nuna damuwa kan rahotannin ƙaruwar hare-haren kyamar baƙi da ake kai wa kan ‘yan kasashen waje.

Related Articles

Leave a Comment

Prove your humanity: 6   +   4   =